الأربعاء، 9 يناير 2019

Kusan rabin 'yan Birtaniya sau daya suke wanka a mako

A wani sabon bincike da aka gudanar a kasar Birtaniya namiji daya cikin maza 25 da mace daya cikin mata 30 sun ce suna yin wanka sau daya a tsahon mako guda.


A wani binciken daban da aka gudanar a shekarar 2011 maza miliyan 1 da dubu dari biyu da mata 960,000 sun ce su kan yi wanka ko watsa ruwa sau daya a tsahon kwanaki bakwai.


An yi binciken ne kan 'yan Birtaniya 2,034 inda aka tambaye su sau nawa suke wanka ko watsa ruwa a mako.


Source: bbc hausa


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق