الأربعاء، 9 يناير 2019

Ana ci gaba da zanga-zanga a wasu biranen Sudan

Bangarori biyu da ke adawa da juna sun yi tattaki a titunan Khartoum, babban birnin Sudan da birnin Omdurman.


Daruruwan mutane ne suka taru a dandalin Green Square don jaddada goyon bayansu ga Shugaba Omar al-Bashir, wanda ke fuskantar kalubale mafi girma a shekaru 30 da ya yi a mulki.

Taron mutanen, wanda yawanci 'yan jam'iyya mai mulki ne da ma'aikatan gwamnati sun taru don karfafa wa shugaban mai shekaru 76 gwiwa.

Kalli hotunan zanga-zanga a Sudan


Likitoci sun shiga zanga-zanga a Sudan


Zanga zangar dalibai a Sudan


Wannan ne jawabin farko da shugaban ya yi a bainar jama'a a Khartoum tun fara zanga-zangar kin jinin gwamnati a garin Atbara da ke arewacin kasar ran 19 ga watan Disamba.

Shugaban ya bayyana ne da matarsa Wedad Babkier, inda ta tsaya daga bayansa.

Ya yi zargin cewa wasu 'yan tada zaune tsaye daga wajen kasar ne ke shirya zanga-zangar, kuma ya yabi rundunar soji da sauran jami'an tsaro kan kokarinsu a yayin zanga-zangar.

A daya bangaren kasar kuwa a birnin Omdurman, ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati mafi girma a kasar.

A watan da ya gabata ne dai aka fara zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin inda har likitocin kasar ma suka shiga zanga-zangar .

Masu zanga-zangar sun kona ofishoshin jam'iyya mai mulki da wasu hukumomin gwamnati.

Kawo yanzu, a kalla mutane goma aka kashe.

Source: bbc hausa

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق