Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa : *«Allah yana da sunaye casa'in da tara, wato dari ba daya, wanda ya kiyaye su zai shiga aljanna.. »*
Mutane da yawa sun dauka cewa kiyaye wadannan sunaye yana nufin haddace su a kwakwalwa, koda ba a san ma'anonin da suka kunsa ba, hakan ya sanya mutane da yawa suka mayar da himma wajen haddace su kawai, da tunanin cewa hakan tamkar wata dama ce ta su yanki ticket din su na shiga aljanna!..
Gaskiyar abin da kalmar "kiyayewa" take nufi a nan ita ce : Sanin ma'anonin wadannan sunaye a matakin farko, sannan kuma a sifantu da wadannan ma'anonin a rayuwar yau da kullum..
Alal misali, a cikin sunayen Allah akwai *"as-Salam",* ma'ana: aminci da natsuwa da zaman lafiya, idan mutum ya kiyaye wannan suna zai zamo wata mabubbuga ce ta zaman lafiya da kwanciyar hankali da aminci ga daukacin halittun Allah Madaukakin Sarki.. Ba zai cutar da dan uwansa mutum ba, ba zai cutar da dabbobi ba, ba zai zamo mai gurbata yanayi ba, ba zai zamo barazana, ko wata alama ta sanya tsoro a cikin zukatan al'umma ba..
A cikin sunayen Allah akwai *"al-afuwwu",* ma'ana: mai rangwame da yafiya da afuwa.. Kiyaye wannan suna yana nufin sifantuwa da wadannan sifofi.. Mutum ya zamo mai amsar hanzari, mai kuma yawan yafiya da hakuri, wani bawan Allah yana cewa : "wanda yake da hanzari kam za mu amshi hanzarinsa.. Wanda kuma ba shi da hanzari, mu da kanmu ne za mu yi masa hanzari.. "..
Haka ma a cikin sunayen Allah akwai *"al-Adlu",* ma'ana : mai adalci, adalci shi ne: sanya komai a inda ya dace, akasin adalci shi ne: zalunci da kama-karya.. Kiyaye wannan suna yana nufin mutum ya zamo mai adalci tsakanin al'umma, kada ya yarda ikon da Allah ya ba shi ya fizge shi zuwa ga zaluntar wani daga cikin halittun, kada ya yarda ta'assubanci ya hana shi yin gaskiya da adalci akan kowa.. Kada kuma ya bai wa makusantansa wani fifiko wajen daukan aiki akan sauran mutane saboda kawai su makusantansa ne, muddin ba su ne suka cika sharuddan da ake bukata sama da kowa ba, Amma idan suka cika sharudda, sam bai kamata ya nesanta makusantan nasa, gudun kada a ce ya yi son kai ba.. Adalci na nufin ajiye abin da ya dace a wurin da ya dace kaman yanda muka fada..
Kiyaye sunayen Allah yana nufin sifantuwa da ma'anonin da suke dauke da su...
*Saleh Kaura*
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق