الأربعاء، 9 يناير 2019

Nijeriya : Mutum Miliyan 84 Zasu Kada Kuri'a A Zaben 2019

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta sanar da cewa sama da 'yan kasar miliyan 84 ne sukayi rejista a babban zaben kasar na watan gobe dake tafe.


Da yake sanar da hakan, ga shugabannin jami'iyyun siyasa yau a Abuja, shugaban hukumar zaben ta INEC, Mahmood Yakubu, ya ce rajista na karshe na masu zaben 2019 ya kama mutum miliyan 84, 004,084.

Yawan masu wadanda suka cancanci yin zaben ya karu da ksuan kashi 20%, idan aka kwantanta da waccen babban zaben kasar da ya gabata a shekara hudu da suka wuce, inda mutum sama da miliyan 68 sukayi rejistar zabe.

Haka zalika a cewar hukumar ta INEC 'yan takara 73 da suka fito daga jam'iyyun siyasa 91 ne zasu fafata a zaben shugaban kasa. ciki harda shugaba mai barin gado Muhammadu Buhari, dake neman wani wa'adin mulki na biyu, inda zai fafata da babban abokin hammayarsa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar. 

Za'a gudanar da zaben 'yan majalisa makwanni biyu bayan zaben shugaban kasa, inda 'yan a majalisar datijai, kujeru 109 ke zawarcin 'yan majalisa, sai kuma 360 daga bangaren majalisar dokoki, sai kuma zaben gwamnani a jihohi 29 daga cikin 36 a fadin kasar ciki harda Abuja babban birnin tarayya.

Hukumar ta INEC ta ce ta dauki kwararen matakai za zaben mai zuwa ciki harda yaki da saida kuri'a, kamar yadda aka gani a zaben jihar Ekiti, da amfani da wayar salula da kuma na'urar daukan hoto.

A ranar 16 ga watan Fabrairu mai zuwa ne al'ummar Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a Nahiyar Afrika zasu kada kuri'a a babban zaben kasar. 

Source: pars today

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق